Sanarwar ta nuna cewa, an fi fama da bala'in a birnin Niamey da jihar Tillabery, inda ambaliyar ruwan ta lalata gonaki da hanyoyin motoci da gadoji da dama.
Sanarwar ta kara da cewa, lamarin zai iya janyo karancin hatsi a kasar Nijer sakamakon bala'in da aka samu a manyan yankunan kasar. Don tinkarar matsalar, gwamnatin kasar ta samar da abinci ton 326 don taimakawa jama'a masu fama da bala'in, kuma tana shirin samar da kudi da fasahohi ga yankunan da bala'in ya shafa. (Zainab)