in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijer ta kaddamar da asibitin da kasar Sin ta gina
2016-08-03 09:51:07 cri
A jiya Talata Shugaban jamhuriyar Nijer Mahamdou Issoufou ya jagoranci kaddamar da katafaren asibitin da kasar Sin ta gina a matsayin gudumowa ga gwamnatin Nijer a birnin Niamey.

Bikin wanda ya samu halartar jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijer Shi Hu, da shugaban majalisar dokokin Nijer Ousseini Tini, da manyan jami'an hukumomin gwamnati, da ministoci, da 'yan majalisun dokokin, da kuma wakilan ofishin jakadanci.

Issoufou, ya bayyana cewar asibitin nada girman daukar gadaje 500, kuma shine asibiti mafi girma dake da kayyayakin aiki irin na zamani a Afrika ta yamma.

Kimanin CFA biliyan 40 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 68 ne aka kashe wajen gina asibitin, kana asibitin yana da girma hecta 16 wanda arewacin Niamey, kuma an gina asibitin ne domin amfanin alummar jamhuriyar Nijer da makwabtan kasashe.

Asibitin ya shafi dukkanin bangarorin aikin jinya, da suka hada da sashen kulawar gaggawa, da sashen kula da ciwon zuciya, da dakunan tiyata 16, da dakunan gwaje gwaje, da sashen adana jini, dana daukar hoto da dai sauransu.

Bugu da kari, asibitin zai iya kasancewa cibiyar bada horo ga ma'aikatan jiyya, kuma zai shafi sauran ayyukan duba marasa lafiya.

Ministan kula da lafiya na jamhuriyar Nijer Kalla Moutari ya bayyana cewar, za'a bada sassauci ga kudaden da marasa lafiya zasu dinga biya. Ana saran wannan katafaren asibiti zai rage kudaden da Nijer ke kashewa a duk shekara sama da CFA miliyan 5 wajen kaiwa marasa lafiya zuwa kasashen waje.

Dangantakar dake tsakanin Sin da Nijer, ya shafi bangarori da dama da suka hada da na siyasa, da tattalin arziki, da makamashi, da tsaro da kuma kayayyakin more rayuwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China