in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a inganta dangantakar abokantaka ta samun bunkasuwa a tsakanin kasa da kasa
2016-10-05 16:31:11 cri
Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana a jiya Talata cewa, aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030 shi ne muhimmin aiki da za a aiwatar a yanzu da ma nan gaba.

A dai wannan rana ne aka gudanar da muhawarar kwamiti na biyu mai kula da batun tattalin arziki na babban taron MDD karo na 71, inda Wu Haitao ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu ci gaba, da kasashe masu tasowa, shi ne muhimmiyar hanya ta raya hadin gwiwar kasa da kasa, kuma kamata ya yi kasashe masu ci gaba su cika alkawarin taimakawa kasashe masu tasowa musamman kasashen Afirka, da kasashe mafiya karancin samun bunkasuwa, da kananan kasashe masu tasowa, kana su taimakawa kasashe masu tasowa wajen inganta karfinsu na samun bunkasuwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China