A jiya Litinin ne, aka rufe muhawara ta babban taron MDD karo na 71 a hedkwatar majalisar dake birnin New York na kasar Amurka.
A madadin babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon, mataimakin babban magatakardan Jan Eliasson ya bayyana kafin rufe taron cewa, an shirya taron muhawara na MDD ne domin nazartar halin da kasashen duniya ke ciki, duk da cewar, ana fama da tsananin zafi, amma muhawarar ta ba da kwarin gwiwa sosai wajen daidaita wannan matsala, ta kuma dasa sabon harsashi ta fuskar bunkasuwa domin cimma burin neman samun dawamammen ci gaba kafin shekarar 2030, kana ta samar da sabon tsarin daidaita batutuwan 'yan gudun hijira da masu nema kaura.
Jan Eliasson ya kuma jaddada cewa, hanyar siyasa ita ce hanya daya tak ta daidaita batun Syria.
A sanarwarsa bayan taron, shugaban babban taron MDD Peter Thomsen ya bayyana cewa, wakilan kasashe daban daban sun bayyana aniyyarsu ta tabbatar da burin neman samun dawamammen ci gaba, inda suka fitar da sanarwa game da batutuwan 'yan gudun hijira da masu neman kaura, tare da bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, rikicin Syria, yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. A cikin sanarwarsa, Peter Thomsen ya yi kira ga bangarori daban daban da su hanzarta fara aiki da yarjejeniyar Paris domin hana karuwar zafi.(Lami)