Shugaba Buhari, a cikin wani jawabi ta kafofin gidajen rediyon kasa, albarkacin cikon shekaru 56 da aka samu 'yancin kan kasar, ya bayyana cewa gwamnati ta bullo da wasu shirye shirye domin tattabar da cewa Nijeriya ta ciyar da kanta ta fuskar abinci.
Ya kara da cewa gwamnati ta kaddamar da wani sabon tsari domin ingiza tattalin arzikin karkara, domin manoman wurin, musammun ma domin sake farfado da noma a yankunan karkara.
Samar da isasshen abinci, musammun ma hatsi, dawa, waken soja, shimkafa, masara na dogaro da aiwatar da wannan tsari, a cewar shugaban Najeriya.
A tsawon wannan sabon tsari, da ma'aikatar noma da cigaban karkara ta tsara, za a samar da karin hatsi a cikin jahohin Najeriya goma sha uku.
Wannan tsari mai taken "Shirin rayuwa" zai sanya Najeriya ta yi tanadin kudaden da take kashewa wajen sayen abinci, in ji shugaba Buhari.
Najeriya za ta kashe a wannan shekara a kalla dalar Amurka biliyan biyu wajen shigo da shimkafa, a cewar hukumomin kasar. (Maman Ada)