Wannan kundi, a cewar wannan sanarwa an bullo da shi ne, domin amsa bukatu daban daban na masu ruwa da tsaki na harkokin kasa da kasa a wannan fanni, da kuma kasancewa daidai da dokokin kasashen na shiyyar ta fuskar shige da fice, musammun na kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS da na kungiyar kasashen yammacin Afrika masu amfani da kudin sefa wato UEMOA.
A cewar gwamnatin Nijar, dokar shekarar 1961 dake tafiyar da aikin kwastan a Nijar tana nuna yawancin rauninta wannan kuma tun bayan shekaru 55 dake ta aiki. Duk da cewa tana nata aiki a wasu fannoni, amma yanzu ba ta da karfin amsa bukatun yanzu na hukumar ma'aikatan kwastan da kuma abokan hulda da kwastan cewa 'yan kasuwa da sauransu. (Laouali Souleymane)