Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma daraktan kwamitin raya kasa da aiwatar da kwaskwarima na kasar Mr. Xu Shaoshi, da firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn, da shugaban kasar Djibouti Ismail Oomar Guelleh, da shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé na cikin mahalarta bikin, sun kuma gabatar da jawabai.
A cikin jawabin sa Mr. Xu ya ce, wannan layin dogo mai amfani da wutar lantarki irin sa na farko da ya ratsa wasu kasashe a nahiyar Afirka, shi ne kuma layin dogo na lantarki mafi tsayi a nahiyar, wanda kuma zai zamo irin mai amfani da wutar lantarki na farko da wani kamfanin kasar Sin ya gina a nahiyar Afirka, bisa tallafin kasar Sin a fannonin ma'aunin fasahohi, da na'urori, da tsarin tattara kudade, da sa ido, da gudanar da ayyuka da dai sauransu.
Layin dogo tsakanin Addis Ababa da Djibouti ya kasance muhimmiyar alama a tarihin raya kasashen biyu. Ita ce kuma muhimmiyar nasara da aka samu a fannin tabbatar da shirin hadin kai a fannoni 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron koli na Johnnesburg na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika da aka gudanar a bara, wadda kuma ta kasance wani muhimmin aiki dake iya alamanta yunkurin hadin kai tsakanin Sin da Afirka game da raya hanyar dogo, da hanyoyin mota, da zirga-zirgar jiragen sama, da bunkasa masana'antu, da kuma hadin kai tsakanin bangarorin biyu wajen samar da kayayyaki. (Bilkisu)