Za a kaddamar da aikin hanyoyin jiragen kasa masu amfani da lantarki na farko a nahiyar Afirka, wato layin dogo da za su hada birnin Addis Ababa na kasar Habasha da kasar Djbouti a yau Talata 5 ga watan nan, aikin da za a gudanar bisa ma'auni da na'urorin kasar Sin.
Wannan aiki dai shi ne aikin layin dogo na lantarki irin sa na farko da kamfanonin Sin za su gina a nahiyar Afirka, kana tsawon layin ya kai kilomita 752.7. An tsara saurin jiragen kasan da zasu rika bin layin dogon ya kai kilomita 120 a kowace sa'a. An kuma zuba jarin da yawan sa ya kai dalar Amurka biliyan 4, yayin da ake kallon aikin a matsayin mai matukar muhimmanci a kasar Habasha.
Kashi 9 cikin 10 na kayayyakin da ake fitarwa ko shigarwa cikin kasar Habasha na bi ne ta hanyar mashigin tekun kasar Djbouti. Don haka bayan an fara amfani da layin dogo na Addis Ababa zuwa Djbouti, tsayin lokacin sufuri da jigila tsakanin biranen biyu zai ragu daga kwanaki 7 wanda ake yi ta hanyar mota zuwa awoyi 10. Hakan zai kuma warware wasu matsalolin jigilar kayayyaki a yankin, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a kasar Habasha baki daya. (Zainab)