Mataimakin shugaban sashen Afirka na kamfanin CRCC Cao Baogang ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa tsawon layin dogon da zasu gina a jihar Ogun dake Kudu maso Yammacin Najeriya, ya kai kilomita 334, kuma za a gudanar da aikin bisa ma'aunin fasahar gine-gine na kasar Sin, kana saurin jirgin kasa da zai yi zirga-zirga a layin dogon zai kai kilomita 120 a kowace sa'a.
Da yake karin haske game da aikin layin dogon, shugaban kamfanin CRCC Meng Fengchao, ya ce aikin ya hada da layin dogo tsakanin Abuja zuwa Kaduna, da hanyoyin jiragen kasa na cikin birnin tarayya Abuja, da hanyoyin jiragen kasa na Lagos, wadanda gaba daya za su kasance tsarin hanyoyin jiragen kasa mai inganci, aikin da kuma zai tallafa ga raya yankunan kasar, da bunkasuwar tattalin arzikin ta a nan gaba.
Game da aikin gina gidaje a kasar Zimbabwe kuwa, mahukuntan kamfanin na CRCC sun bayyana cewa, aikin zai shafi birane da garuruwan kasar 12, kuma za a gina sabbin gidaje 22,652, a wani mataki na kyautata rayuwar jama'ar kasar kimanin su dubu 100, cikin babban shirin inganta rayuwar jama'a na gwamnatin kasar ta Zimbabwe. (Zainab)