Bisa kididdigar da aka yi, an nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2015, yawan tsawon hanyoyin jiragen kasa na kasar Sin ya kai kilomita dubu 121, ciki kuma wadanda mafi sauri sun kai kilomita dubu 19, wato ya wuce kashi 60 cikin dari bisa na duk duniya baki daya, hakan kasar ta kasance kasa da ta fi samun saurin ci gaban jiragen kasa mafi sauri a duniya.
A nasa bangare, mataimakin babban manajan kamfanin jiragen kasa na kasar Sin Lu Chunfang ya ce, a shekarar 2015 yawan mutanen da suka yi zirga-zirga ta hanyar jiragen kasa ya kai miliyan 2500, nauyin kayayyakin da aka yi jigilar da su ta jirgin kasa ya kai ton miliyan 3360, hakan ya sa kasar ta kai matsayin farko a duniya a fannin. Yanzu kasar Sin tana da fifiko a fannonin fasahohi, tsaro, farashi da dai sauransu, hakan ta samu amincewa sosai daga kasuwar jiragen kasa ta duniya. (Bilkisu)