Bisa hasashen da aka yi, an ce, a wannan shekara ana saran yin jigilar fasinjoji miliyan 332, zuwa sassan kasar ta jiragen kasa domin bikin baraza, wanda ya karu da miliyan 37 da dubu 550, wato karuwar kashi 12.7 cikin dari bisa na shekarar bara.
A shekarar bara, tsawon sabbin hanyoyin jiragen kasa da Sin ta gina ya kai kilomita 9531, inda ta gina kilomita 3306 na hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya. Wannan ya taimaka wajen inganta jigila ta jiragen kasa a kasar Sin, matakin da ya saukaka zirga-zirgar fasinjoji a shekarar bana. (Zainab)