in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRCC ya samu ayyukan gyara manyan hanyoyin jiragen kasa a kasashen yammacin Afirka
2015-12-29 10:24:18 cri
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin CRCC na kasar Sin ya daddale yarjejeniyoyin gyara hanyoyin jiragen kasa tsakanin Dakar na kasar Senegal da kuma Bamako a kasar Mali tare da hukumomin jiragen kasa na kasashen Senegal da Mali, a kan kimanin kudin Sin RMB Yuan biliyan 17.6.

Tsawon hanyoyin jiragen kasan tsakanin Dakar da Bamako sun taso ne daga birnin Dakar na kasar Senegal, inda suka ratsa garuruwan Thies, Diourbel, Tambacounda na Senegal, da Kayes na kasar Mali, kana suka dire a birnin Bamako na kasar Mali, ya kai kilomita 1286.

Tsawon hanyoyin jiragen kasan dake Segenal ya kai kilomita 645, kuma zai lashe kimanin dala biliyan 1.2, kwatankwacin kudin Sin RMB Yuan biliyan 8.1. yayin da tsawon hanyoyin jiragen kasan dake kasar Mali da ya kai kilomita 641, zai lakume kudin da ya kai dala biliyan 1.5, kwatakwacin kudin Sin RMB Yuan biliyan 9.5. kamfanin CRCC na kasar Sin kamfani shi kadai ne ya ke tsarawa tare da gudanar da wadannan ayyukan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China