in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: Sanya kudin RMB cikin SDR zai taimakawa tattalin arzikin duniya
2016-10-06 12:12:19 cri
Mataimakin babban darektan asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Zhang Tao ya ce, sanya kudin kasar Sin na RMB cikin kudaden ajiya na ketare(SDR) da asusun ya yi, yana da matukar muhimmanci ga kasar Sin da ma tattalin arzikin duniya baki daya.

Mr Zhang wanda ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi a wani dandali na cibiyar tattalin arziki ta kasa da kasa da harkokin kudi na kasar Sin ko China finance 40 ta Peterson da ke Washington, ya ce, sanya kudin na RMB cikin wannan tsari, ya nuna yadda a 'yan shekarun nan ake amincewa da amfani da kudin a ckin tsarin kudade na duniya, kamar yadda aka tsara a manufofin yin gyare-gyare na kasar da nufin cimma manufar kasar ta komawa ga tsarin tattalin arziki da zai kara bude kofofinsu ga duniya.

A cewar Zhang, sanya kudin na RMB cikin wannan tsari, zai kara masa farin jini da samun karbuwa a duniya, zai kuma ba da tasa gudummawa wajen rage dogara kan wasu kudade.

Wannan yana nuna cewa, mambobin asusun na IMF za su iya amfani da kudin kasar Sin na RMB wajen tafiyar da harkokin asusun. A takaice dai kudin na RMB ya zama wata kafa ta magance duk wani rikicin kudi da ka iya kunno kai a nan gaba.

A watan Nuwamban da ya gabata ne, asusun IMF ya yanke shawarar sanya kudin kasar Sin cikin jerin kudaden ajiya na ketare(SDR) inda ya kasance kudi na biyar,wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Oktoban wannan shekara a hukumance. Wannan shi ne karon farko da asusun IMF ya sanya wani kudi daga kasa mai tasowa a cikin wannan tsari. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China