Rahoton ya bayyana cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasashe masu ci gaba bai karu sosai ba, ko da yake yawan na sabbin kasashe mafiya samun ci gaban tattalin arziki, da kasashe masu tasowa ya zarce zaton da aka yi, kuma IMF din ya tabbatar da hasashen sa game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Rahoton ya daga zaton saurin bunkasuwar tattalin arzikin sabbin kasashe mafiya samun ci gaban tattalin arziki, da kasashe masu tasowa da kashi 0.1 cikin dari, wato adadin ya kai kashi 4.2 cikin dari, wanda ya zarce yawan na shekarar 2015, wanda ya tsaya a kashi 4 cikin dari. Kuma wannan ne karo na farko da aka daga matsayin hasashen a cikin shekaru 6 da suka gabata.
Rahoton ya yi hasashen cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin a bana da badi bai canja ba, wato kashi 6.6 cikin dari, da kuma kashi 6.2 cikin dari. (Zainab)