An dai tsare mutanen biyu ne a ranar Laraba, bayan 'yan sanda sun gayyace su wata tattaunawa a garin Luanshya dake lardin Copperbelt cikin makon da ya gabata.
'Yan sandan sun bukaci mutanen biyu su bada bahasi game da kalaman da suka furta, yayin da suka ziyarci wasu 'yan jam'iyyar su dake tsare a garin na Luanshya tun bayan babban zaben kasar na watan Agusta.
Kwamishinan 'yan sandan Copperbelt Charity Katanga ya tabbatar da tsare mutanen biyu, bisa zargin yunkurin tunzura magoya bayan su, cikin wani jawabi da suka gudanar a ranar 26 ga watan Satumbar da ya gabata.(Saminu)