in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki Moon ya bukaci 'yan siyasar Zambia da su warware sabani cikin lumana
2016-08-16 20:38:54 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya taya al'ummar kasar Zambia murnar kammala babban zaben kasar cikin lumana, tare da bukatar daukacin 'yan siyasar kasar, su dauki matakan warware dukkanin sabanin da ka iya biyo bayan zaben, bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

Kalaman na Mr. Ban dai na zuwa ne bayan da aka ayyana sunan shugaban kasar ta Zambia mai ci wato Edgar Lungu, a matsayin wanda ya lashe zaben, ko da yake dai 'yan adawa na zargin an tafka magudi a yayin zaben, don haka suka ce za su kalubalanci sakamakon da aka bayyana.

A ranar Alhamis din makon jiya ne al'ummar Zambia suka kada kuri'u a zaben shugaban kasa, da na 'yan majalissu, tare da na wakilan kananan hukumomi.

Masu sanya ido daga kasashen Afirka dai sun ce an gudanar da zaben lami lafiya, ba kuma tare da wani magudi ba, duk kuwa da cewa an ci karo da 'yan matsaloli nan da can.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Shugaban Zambiya Edgar Lungu ya yi tazarce 2016-08-16 10:05:35
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China