in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaurara matakan tsaro a Zambia gabanin rantsar da shugaba Lungu
2016-09-13 09:31:45 cri
Rundunar 'yan sandan kasar Zambia ta bayyana cewa, an tsaurara matakan tsaro a fadin kasar gabanin rantsar da shugaba Edgar Lungu da aka sake zaba.

Sipeto janar na 'yan sandan kasar Kakoma Kanganja ya ce, an dauki wannan mataki ne don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yayin bikin,yana mai cewa, duk wanda ya yi yunkurin kawo nakasu ga wannan biki to kuwa zai yabawa aya zaki.

Babban jami'in 'yan sandan ya kara da cewa, an haramta shiga filin bikin rantsar da shugaban kasar da kwalabe ko jakakkuna duk da nufin kara daukar matakan tsaro.

A daya hannun kuma, hukumar kiyaye hadurra ta kasar Zambia ta fitar da wata sanarwa a yau Talata cewa, jami'anta a sassa daban-daban na kasar za su kasance cikin shirin kota-kwana don tabbatar da tsaro ga masu ababan hawa. Tuni kuma mahukuntan kasar ta Zambia suka ayyana yau Talata a matsayin ranar hutu, don baiwa jama'a damar bibiyar bikin rantsar da shugaban kasar wanda kuma za a nuna shi kai tsaye ta manyan allunan talabijin da aka kafa a manyan biranen lardunan kasar.

Rahotanni na cewa, tun daga watan Janairun shekarar 2015 zuwa wannan lokaci ne shugaba Lungu ya ke jagorantar kasar Zambia, bayan da ya lashe zaben shugaban kasar da aka kira sakamakon mutuwar tsohon shugaban kasar marigayi Micheal Sata a shekarar 2014. Sai dai 'yan adawa sun ce an tabka magudi a zaben na ranar 11 ga watan Agustan da ya gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China