in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta taya wa Esther Lungu murnar lashe zaben shugaban kasar Zambia
2016-08-20 13:02:51 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang a jiya Jumma'a ya bayyana cewa, kasar Sin ta taya wa Esther Lungu murna saboda kara ci zaben shugaban kasar Zambia da ya yi.

Mista Lu ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka saba yi a ranar Jumma'a. Bisa tambayar da aka masa cewa, a ranar 15 ga watan Agusta ne, hukumar zaben Zambia ta sanar da cewa, shugaban kasar na yanzu Esther Lungu ya lashe zabe bisa yawan kuri'un da ya samu na kashi 50.35 cikin 100, ko mene ne ra'ayin kasar Sin kan wannan batu?

Mista Lu ya amsa cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, a karkashin shugabancin shugaba Lungu, gwamnati da jama'ar kasar Zambia za su samu sabbin manyan nasarori wajen raya kasarsu.

A cewar Lu, kasar Zambia abokiya da kuma 'yar uwar kasar Sin ce a nahiyar Afirka. Kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan zumuncin da ya dade yana kasacewa tsakaninta da Zambia, da kuma ci gaban dangantakar a tsakanin bangarorin biyu. Sin tana kuma fatan yin kokari tare da Zambia, domin karfafa dangantakar hadin kai ta abokantaka a tsakaninsu, don amfanawa jama'ar kasashen biyu.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China