in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon shugaban kasar Zambiya Kaunda yayi kira ga zaman lafiya bayan zabukan dake cike da takadama
2016-08-26 10:31:54 cri
Tsohon shugaban kasar Zambiya, Kenneth Kaunda, yayi kira a ranar Alhamis ga zaman lafiya bayan zabukan dake cike da takadama da suka janyo tashe tashen hankali da hare haren kabilanci a cikin wasu yankunan kasar.

Mista Kaunda, da ya jagoranci kasar Zambiya tun bayan samun 'yancin kanta daga kasar Burtaniya daga shekarar 1964 zuwa 1991, yayi kiran al'ummar kasar dasu rungumi zaman lafiya a cikin lokuta na bayan zabe, da kuma rike kauna tsakaninsu.

Mai shekaru 92 da haihuwa, mista Kaunda ya bayyana a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Bole dake birnin Addis Abeba, cewa makomar Zambiya tana hannun Allah, a cewar wata sanarwar ofishin jakadancin Zambiya dake kasar Habasha.

Tsohon shugaban kasar Zambiya ya yada zango a Habasha bisa hanyarsa ta zuwa Guinee Equatoriale inda zai halarci wani dandali tare da wasu tsoffin shugabannin kasashen Afrika guda talatin domin tattauna makomar Afrika.

Zabukan Zambiya na ranar 11 ga watan Augusta sun kammata tare da tashe tashen hankali a wasu sassan kasar tsakanin magoya bayan shugaban kasa mai barin gado Edgar Lungu, da kuma magoya bayan babban dan adawa, Hakainde Hichilema.

Wadannan tashe tashen hankali sun barke, bayan sanar da nasarar shugaba Lungu a zaben shugaban kasa.

Shugabannin biyu sun yi kira ga magoya bayansu dasu maido da zaman lafiya, amma duk da haka, mista Lungu ya ki amincewa da ya gana tare da shugaban 'yan adawa domin tattaunawa kan al'amuran da suka girgiza kasar.

Mista Hichilema yayi watsi da nasarar mista Lungu gaban kotun kolin kasar, tare da tilastawa gwamnati soke shirye shiryen bukukuwan rantsar da misat Lungu a wannan mako. Mista Lungu ya lashe zaben shugaban kasa da kuri'u 1,860,877 gaban abokin takararsa mista Hichilema wanda ya sami kuri'u 1,760,347. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China