in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Aston Villa da wani basine ya saya ta sallami manajanta
2016-10-05 13:57:55 cri
Kungiyar Aston Villa ta kasar Birtaniya, wadda ke buga gasar Championship ta kasar Ingila, ta sallami manajanta Roberto Di Matteo a ranar Litinin. An dai sallami kocin ne a sakamakon yadda kungiyar ta gaza cimma nasarar lashe wasannin da ta buga, lamarin da ya kai ta sauka matsayi na daf da kasan teburin gasar ta Championship.

Mai wannan kungiyar dai wani Basine mai suna Dr. Tony Xia, wanda ya ware kudi da yawan su ya kai dalar Amurka fiye da miliyan 64, a lokacin zafi na bana don sayen kulob din na Aston Villa, tare da burin sake daga matsayin kungiyar ta yadda zai koma buga gasar kuloflika mafiya kwarewa a Birtaniya wato Premiership.

Sai dai sakamakon da kungiyar ta samu a wannan kakar wasa bai dace da burin mista Xia ba ko kadan, musamman ma yadda Preston ya lashe Aston Villa da ci 2 da ba ko daya, a wasan da suka buga a ranar Asabar din da ta gabata, sakamakon da ya sanya gibin dake tsakanin kungiyar Aston Villa da Huddersfield, wadda ke saman teburin gasar Championship ya kai ga maki 15. Hakan ya sa Aston Villa sauka zuwa matsayi na 19, ta yadda idan ta sake rasa maki 2 a wasannin ta na gaba, za ta fada relegation ke nan.

Kulob din Aston Villa, wanda ke yankin Midlands na tsibirin England, ya sanar da sallamar kocin na sa a shafin sa na yanar gizo, inda ya ce Steve Clarke zai zama manajan kungiyar na wucin gadi, yayin da ake kokarin nemo wani kwararre da zai karbi jagorancin kungiyar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China