in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaman makarantu a Senegal sun janye yajin aikin da suka shiga
2016-06-15 20:12:56 cri
Yanzu haka malaman makarantu a kasar Senegal sun dakatar da yajin aikin da suka tsunduma a ciki,sakamakon rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin gwamnati da kungiyoyin malaman kasar.

Kungiyoyin dai sun amince su dakatar da yajin aikin ne,bayan da shugabanin addinai a kasar suka shiga tsakani.

Tun a cikin watanni hudun da suka gabata ne, aka fara samun takun-saka a bangaren Ilimin kasar sakamakon gazawar gwamnati na cika alkawarin da ta yiwa malaman na biyansu albashi da kudadensu na alawus-alawus.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China