in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin sa hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar al'adun kasar Sin a Senegal
2016-06-18 13:30:43 cri
Jiya Jumma'a a birnin Dakar, an shirya bikin sa hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar al'adun kasar Sin a kasar Senegal a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, inda jakadan kasar Sin dake Senegal Zhang Xun, da ministan kula da harkokin wajen kasar Senegal Mankeur Ndiaye sun halarci bikin, tare da sanya hannu kan yarjejeniyar.

A cikin jawabinsa, mista Ndiaye ya ce, a yanzu haka hadin kai dake tsakanin kasashen Senegal da Sin ya kai wani babban matsayin da ba a taba ganin irinsa ba a da, ayyukan hadin kansu na shafar noma, aikin kamun kifi, tattalin arziki, fasahohi da kuma ababen more rayuwa da dai sauransu. Ministan ya ce, kasar Sin na da dogon tarihin wayin kai, likitancin gargajiyar kasar Sin, abincin Sin, fasahar rubutu, ra'ayin Confucius da kuma sauransu dukkansu kayan tarihi ne da Sin ta kiyaye wa duniya. Cibiyar al'adun kasar Sin a Senegal da za a kafa za ta samar da wani dandali mai kyau wajen yin cudanyar juna tsakanin al'adun Sin da Afirka.

A nasa bangare, jakada Zhang Xun ya bayyana cewa, a shekarun baya, an yi ta yin cudanyar al'adu a tsakanin kasashen Sin da Senegal, kuma an samu manyan nasarori. An cimma nasarar kafa babban ginin nuna wasannin fasaha bisa taimakon da Sin ta bayar, da gidan ajiye kayayyakin gargajiya na wayin kan bakar fata, da kwalejin Confucius na jami'ar Dakar daya bayan daya, hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta sha'anin al'adun Senegal, da karfafa yin cudanya tsakanin al'adun kasashen biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China