Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun, ta bayyana cewa Najeriya ta fara farfadowa daga matsalar tattalin arziki da ta fada, sakamakon wasu managartan matakai da gwamnatin kasar mai ci ke aiwatarwa.
Adeosun ta bayyana hakan ne ga manema labarai, tana mai cewa nauyin aiwatar da wadannan matakai ya rataya ne a wuyan daukacin sassan kanana da manyan hukumomin gwamnatin kasar. (The Guardian)