Sanarwar ta nuna cewa, wadannan kudade za su tallafawa shirin sufuri da bunkasa ababen more rayuwa a birane (PTDIU), kuma makasudinsa shi ne na kyautata zirga zirga da samar da ababen more rayuwa a yankunan karkara da birane da aka tantance, inda a lokacin rikici ko matsalar gaggawa, za a iya mayar da martani mai nagarta cikin gaggwa.
Shirin zai cike kokarin da gwamnatin kasar ta yi wajen samar da kudaden gine gine, kana zai taimaka wajen rage gibin ababen more rayuwa a tsakanin manyan biranen kasar da aka tantance.
Sanarwar ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen hade yankunan noma da yankunan masu bukata, ta yadda zai aza tushen kyakkyawar dangantaka tsakanin yankunan dake nesa da manyan birane
Wannan shirin dake kunshe da bangarori daban daban zai kasance a karkashin jagorancin babban ofishin da ke kula da harkokin sufuri na Burkina Faso kuma aiwatar da shi zai tsaye a hannun ma'aikatu daban daban da suka samu gajiyar shirin. (Maman Ada)