Da yake magana a ranar Alhamis a yayin wani taron manema labarai, mista Thieba ya nuna cewa adadin wannan kudi na PNDES ya tashi zuwa fiye da Sefa biliyan 15,395, wanda ya tashi fiye da Sefa biliyan 3,079.1 a kowace shekara.
Bisa tanade tanaden da suka shafi wadannan kudade, gwamnatin Burkina Faso na ba da muhimmanci ga albarkatun cikin gida da aka kiyasta zuwa kashi 63,8 cikin 100, kimanin Sefa biliyan 9,825.2, in ji Thieba.
Faraministan ya jaddada cewa burin wannan tsarin ci gaba na shugaban kasa Roch Marc Christian Kabore shi ne na wuce kashi 6.2 cikin 100 na bunkasuwar shekara bisa matsakaici ta shekaru goman da suka gabata, zuwa a kalla kashi 8 cikin 100 a kowace shekara, a tsawon wa'adin mulkinsa na gaba, domin rage matsalar talauci da kashi 40 cikin 100 zuwa a kalla kashi 35 cikin 100 nan da shekarar 2020. (Maman Ada)