in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burkina Faso na ziyarar aiki ta farko a Cote d'Ivoire
2016-07-29 11:31:19 cri

Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya isa Yamoussoukro, hedkwatar mulkin kasar Cote d'Ivoire a ranar Alhamis, bisa tsarin wata ziyarar aiki ta farko a wannan makwabciyar kasa.

A Yamoussoukro, mista Kabore zai jagoranci tare da takwaransa na Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, wani dandalin jarjejeniyar abokantaka da dangantaka (TAC) karo na biyar tsakanin kasashen biyu, in ji wata majiya mai tushe a ranar Alhamis.

A cewar wata sanarwar fadar shugaban kasar Burkina Faso, wannan haduwa ta wannan dandalin da za a bude a ranar Jumma'a, za ta kasancewa wata babbar dama ga shugabannin biyu wajen yaukaka dadadar dangantakar dake hada Cote d'Ivoire da Burkina Faso, da kuma cusa wani sabon karfi ga huldar dangantakarsu.

Haka kuma, za a dauki manyan matakai a yayin wannan dandali, lamarin dake bayyana niyyar shugabannin kasashen biyu na kara fifita moriyar al'ummomin kasashen biyu a ko da yaushe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China