Shugaban Burkina Faso yayi kira ga jama'a dasu harlarci taimakon ba da jini sosai
Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya gayyaci 'yan kasarsa da su halarci taimakon bada jini sosai domin ceto rayukan mutane. A kasar Burkina Faso, bukatar da ake da ta jini ta wuce taimakon jinin da ake badawa. Dalilin hake ne, ya dauki wannan mataki, kira ne zuwa ga dukkan 'yan Burkina Faso na ganin cewa ko wadanne watanni uku, an je an yi kyautar jini, ga mata ko wadanne watanni hudu, haka kuma mutane masu shekaru 18 zuwa 60 duk sun cancanci bada jinin, in ji shugaban Burkina Faso. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku