in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Syria sun sanar da karshen kwanaki 7 na tsagaita bude wuta
2016-09-20 10:55:33 cri
Jiya Litinin 19 ga wata, sojojin gwamnatin kasar Syria sun sanar da cewa, an riga an kawo karshen kwanaki 7 na tsagaita bude wuta, kuma suna zargin dakarun masu dauke da matamai da sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta har sau da dama cikin wadannan kwanaki 7 da suka gabata.

A wannan rana, sojojin gwamnatin kasar Syria sun fidda wata sanarwa, inda suka bayyana cewa, ko da dakarun sun keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta har sama da sau 300 cikin wadannan kwanaki 7 na tsagaita bude wuta, amma, sojojin gwamnati sun yi ta dukufa wajen kai zuciya nesa, yayin da suke mai da martani kan wasu hare-haren da dakarun suka kai.

A sa'i daya kuma, bisa labarin da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na Syria, an ce, cikin ranar da aka fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar, sojojin gwamnatin kasar Syria sun harbe dakaru kimanin 30 a yayin da suke mai da martani kan harin da dakarun kungiyar adawa da gwamantin ta kai, daga bisani kuma, sojojin gwamnati sun kashe dakaru da dama a yayin da suka mai da martani kan wasu hare-haren da dakarun adawa da gwamnati suka tayar a wasu sansanonin sojojin gwamnatin dake arewacin lardin Aleppo.

Haka zalika, kungiyar sa ido kan harkokin hakkin dan Adam ta kasar Syria wadda hedkwatarta take birnin London na kasar Burtaniya ta bayyana cewa, a wannan rana kuma, an kai hari ga wata tawagar motocin dake dauke da kayayyakin agajin jin kai a birnin Aleppo, lamarin da ya haddasa rasuwar ma'aikata 12 na wannan tawaga.

Bugu da kari, kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka John Kirby ya fidda wata sanarwa a jiya Litinin cewa, cikin wadannan kwanaki 7 na tsagaita bude wuta, hare-haren dake tsakanin bangarorin da rikicin kasar ya shafa sun ragu, amma ba a samu yin jigilar kayayyakin agajin jin kai kamar yadda ake fata ba. Shi ya sa, kasar Amurka tana son tsagaita wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sa'an nan za ta ci gaba da yin shawarwari da kasar Rasha kan batun Syria, kana, ya nuna fatan cewa, kasar Rasha za ta nuna matsayinta kan ko ya dace a ci gaba da tsawaita yarjejeniyar din ta tsagaita wuta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China