in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan gwamnatin Sham ta janye daga wata muhimmiyar hanyar mota dake Aleppo
2016-09-16 12:20:41 cri

Majiyar rundunar sojin gwamnatin kasar Sham, ta bayyana a jiya Alhamis 15 ga watan nan cewa, da yammacin wannan rana sojojin gwamnatin kasar sun fara janyewa, daga hanyar mota ta Castello da ke garin Aleppo a arewacin kasar, sun kuma mika ikon yin amfani da hanyar ga rundunar sojan kasar Rasha, domin bada damar jigilar kayayyakin jin kai zuwa yankin da ke hannun 'yan hamayya a gabashin Aleppo.

Majiyar ta kara da cewa, bayan da rundunonin sojan Sham da Rasha suka yi musayar ikon hanyar mota ta Castello, za a yi amfani da hanyar wajen ba da taimakon agaji ne kadai.

Ana sa ran a yau Jumma'a, ta wannan hanya wani ayarin motoci masu dauke da kayan taimako karkashin shugabancin MDD, zai shiga yankin da ke hannun 'yan hamayya a gabashin Aleppo. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China