Manzon musamman na MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura ya shaidawa taron manema labarai da aka kira sa'o'i 24 bayan fara aiki da shirin tsagaita bude wutan a kasar cewa, tashe-tashen hankula sun ragu matuka a kasar. Ko da ya ke wasu rahotanni na cewa, har yanzu ana samun tashin hankali a wasu sassan kasar.
Bugu da kari, jami'in na MDD ya shaidawa manema labarai cewa, tawagar MDD ta shirya kai kayan agaji zuwa yankunan kasar da aka yiwa kofar rago. Amma kuma har yanzu ba a samu izni daga mahukuntan Syria ba.(Ibrahim)