in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bada gudummawa wajen sa kaimi ga farfado da cinikin kasa da kasa
2016-10-02 13:52:31 cri
Game da ganin yadda hukumar WTO ta rage saurin bunkasuwar cinikin duniya a kwanakin baya, kakakin ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa hakan shi ne rashin samun farfadowar tattalin arzikin duniya, kuma kasar Sin tana ci gaba da bada gudummowa a wajen sa kaimi ga farfado da cinikin kasa da kasa.

A ranar 27 ga watan Satumba, hukumar WTO ta gabatar da rahoton zaton bunkasuwar ciniki, inda ta rage zaton bunkasuwar cinikin kayayyaki na duniya daga kashi 2.8 cikin dari da aka tsara a watan Afrilu zuwa kashi 1.7 cikin dari, domin bunkasuwar tattalin arziki da cinikin kasashe masu tasowa kamar Sin da Brazil da sauran kasashe ta sassauta, da yawan kayayyakin da kasashen arewacin nahiyar Amurka ke shigowa ya ragu.

Dangane da batun, kakakin kasar Sin ya bayyana a jiya Asabar cewa, hukumar WTO ta yi tsammani akwai wasu dalilai ne da suka sa raguwar saurin bunkasuwar cinikin kayayyakin duniya. Rashin samun farfadowar tattalin arzikin duniya shi ne muhimmin dalili, kana kasuwar hada-hadar kudi ta duniya ta kawo rashin tabbas ga farfadowar cinikin duniya, ra'ayin yaki da yin cinikin duniya ya kawo tasiri ga kasa da kasa wajen daidaita manfofin ciniki, da kuma yadda aka sake samun ra'ayin bada kariya ga ciniki.

Kakakin ya yi nuni da cewa, bayan rikicin hada-hadar kudi, Sin tana ci gaba da bada gudummowa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da farfado da cinikin kasa da kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China