in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara habaka cinikayyar aikin hidima
2016-05-23 20:15:41 cri

Wani jami'i a ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ya bayyana wajen taron manema labaru da aka kira a ranar Litinin, game da taron cinikin aikin hidima na kasa da kasa karo na 4 da za a gudanar a birnin Beijing na kasar Sin cewa, a yayin da ake gudanar da shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 13, kasar Sin za ta dauki matakai don samun ci gaba a fannin cinikayyar aikin hidima.

Ban da wannan kuma, za a gudanar da taron koli na cinikayyar aikin hidima na duniya karo na farko a yayin wannan taron.

Za a gudanar da taron cinikin aikin hidima na kasa da kasa karo na 4 na birnin Beijing na kasar Sin a ranar 28 ga wannan wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China