in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin daidaita harkokin cinikayyar ketare
2016-08-17 13:53:51 cri
Majalisar gudanarwar kasar Sin ta bukaci kananan hukumomi a matakai daban-daban na kasar, da su kara kokari don daidaita harkokin shigi da ficin kasar wadanda suka fuskanci koma baya a cikin watanni 7 na farkon wannan shekara.

Wannan kira yana kushe ne cikin wata sanarwa da majalisar gudanarwar kasar ta fitar bayan kammala zamanta wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta. Tana mai cewa, kamata ya yi a yi koyi da matakan da shiyyoyin cinikayya marasa shinge na kasar suka bullo da su, wajibi ne kuma a hade dokokin da suka shafi kwastan, haka kuma ya kamata a sassauta ka'idojin duba kayayyaki.

Sanarwar ta kara da cewa, kamata ya yi gwamnati ta yi na'am da irin rawar da masu zuba jari suke takawa wajen bunkasa cinikayyar ketare,kana su kara karfin shiyoyi tsakiya dana yammacin kasar ta yadda za su iya karbar ayyukan da suka shafi harkokin cinikayya.

A farkon wannan watan ne hukumar kwastan ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni 7 na farkon wannan shekara, cinikyayyar ketare na kasar ta ragu da kaso 3 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar bara, inda kayayyakin da ake fitarwa zuwa ketare ya ragu da kaso 1.6, yayin da kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar suka ragu da kaso 4.8 cikin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China