in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cinikin shige da fice a fannin hidima na Sin zai kai dala biliyan 1000 kafin 2020
2016-05-24 12:25:35 cri

Darektar hukumar kula da cinikayya a fannin ayyukan ba da hidima tsakanin kasa da kasa ta ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Qiu Lixin, ta furta cewa, nan da shekara ta 2020, yawan cinikin shige da fice a fannin ayyukan ba da hidima na kasar Sin zai kai fiye da dalar Amurka biliyan 1000, kana matsakaicin yawan karuwarsa zai kai fiye da kashi 10 cikin dari a kowace shekara, wanda zai ci gaba da karuwa a cikin yawan cinikayya da kasar Sin ke gudanarwa tsakanin ta da sauran kasashen duniya. Kaza lika hakan zai karu a mizanin yawan cinikayya ta duniya.

Qiu Lixin ta bayyana hakan ne a jiya Litinin, a gun taron manema labaru na taron cinikayya wajen ba da hidimma na kasa da kasa karo na 4 da ya gudana a nan birnin Beijing. Madam Qiu ta kara da cewa, galibi a aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13 a kasar Sin, ana samar da kyakkyawan muhalli ga bunkasuwar cinikayyar ba da hidimma. Hakan kuwa ya shafi fannin bunkasa tsarin sana'o'i, da kuma fannin yawan kwararru, da fasahohin da kasar Sin take da su, wanda hakan zai yi matukar bunkasa cinikayyar ba da hidimma.

Bugu da kari, an ba da labari cewa, za a yi taron cinikayya na birnin Beijing daga ranar 28 ga watan nan, zuwa ranar 1 ga watan Yuni, a cibiyar taro ta kasar Sin, inda za a mai da hankali kan batutuwan ingnata fasaha da yanar gizo, da fasahar sadarwa, da al'adu, da tarbiyya, da hada-hadar kudi, da kasuwanci, da yawon shakatawa, da kuma kiwon lafiya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China