in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taro na uku na dandalin cinikayya na birnin Guangzhou karo na 119
2016-05-02 12:59:11 cri

An bude taro na uku na dandalin cinikayya na birnin Guangzhou karo na 119 a Jiya Lahadi 1 ga watan nan na Mayu, inda sashen masu shirya dandalin suka bayyana cewa, taruka na farko da na biyu da aka gudanar sun zarce hasashen da aka yi a baya.

An ce duk da cewa yawan 'yan kasuwa mahalarta wannan dandali sun ragu a shekaru 3 da suka gabata, a daya hannun raguwar ba ta karuwa a yanzu haka. Wasu wakilan kamfanonin da suka halarci dandalin karo na farko sun yi hasashen kyakkyawar makoma ga cinikayyar kasar Sin.

Bisa kididdigar da mashirya dandalin suka fitar, yawan 'yan kasuwa da suka halarci taron a karon farko da na biyu sun kai dubu 152, adadin da ya karu da 0.47 cikin dari bisa na mahalarta dandalin a karo na 117. Kaza lika raguwar yawan 'yan kasuwa daga kasashen waje dake halartar taron ita ma a yanzu haka ta tsagaita.

A ganin wasu kamfanoni, mai yiwuwa ne raguwar ta tsagaita ne saboda irin kokarin kyautata tsari, da kirkire-kirkire, da inganta karfin da kamfanonin Sin ke gudanarwa ne a shekarun baya bayan nan. Ko kuma tasirin manufofin kyautata tsarin cinikayya da kasashen waje da kasar Sin ta gabatar, matakan da suka haifar da sauki, da kara imanin nasara game da kamfanonin kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China