A cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a yayin da mazauna wurin suke share fagen maraba da bikin karamar sallah, maharan sun kaddamar da harin ta'addanci, wannan ya girgiza shi sosai.
Ban Ki-moon ya yi kira ga jama'ar Iraki da su yaki kowane irin yunkurin jefa tsoro da wargaza hadin kansu, sannan ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta cafke wadanda suka aikata laifin tun da wuri.
A nasa bangare, mista Lykketoft ya bayyana a sanarwar cewa, wannan harin ta'addanci ya haddasa mutuwar fararen hula da yawa, ciki har da yara kanana da dama, kamata ya yi a yi suka kan wannan hari da babbar murya. Ya ce, MDD za ta hada kanta da jama'a da gwamnatin Iraki domin yaki da ta'addanci.
A jiya wani jami'in Iraki ya furta cewa, a safiyar wannan rana, an kai harin tagwayen boma-bomai da aka dasa cikin mota a birnin Bagadaza, wadanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 126, yayin da wasu 147 suka jikkata. (Fatima)