Shugaban majalisar dokokin Burundi, Pascal Nyabenda a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa, majalisar dokokin Burundi, a matsayinta na mai wakiltar al'ummar Burundi, ta goyi bayan gwamnatin Burundi domin yin watsi da dukkan matakan wannan kuduri mai lamba 2303 dake tsokaci kan tura duk wata runduna a kasar Burundi.
Mambobin majalisar wakilan jama'ar Burundi sun yi watsi musammun ma da aya mai lamba 17 ta wannan kuduri dake bukatar kasashe mambobi na shiyyar da su bada izinin 'yancin zirga zirga ba tare da matsala ko jinkiri ba, daga inda suka fito da kuma shiga Burundi, ga dukkan ma'aikatan dake kunshe da tawagar 'yan sandan MDD a kasar Burundi, har ma da dukkan kayayyakinsu, abincinsu da kayayyaki da aka kebe domin ayyukan musammun na wannan tawagar 'yan sandan MDD.
'Yan majalisar sun bayyana cewa suna damuwa sosai da halayyar wasu mambobin kwamitin sulhu dake kirkiro wasu kudurori kan kasar Burundi ba tare da yin la'akari da ra'ayin kasar Burundi ba, ko ma matakan wasu kungiyoyin MDD, da ma matsalar kasar a halin yanzu. A cewar wannan sanarwa, yanzu lokaci ne na neman wata hanyar sulhunta rikici mai karfi da dorewa na tashe tashen hankalin dake karuwa, wadanda suke janyo tashe tashen hankali ga jama'ar Burundi tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kanta. (Maman Ada)