in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta bayyana kin amincewa kan tura 'yan sandan MDD 228 a kasarta
2016-08-04 09:53:50 cri
Kasar Burundi ta bayyana a ranar Laraba, cikin wata sanarwa, cewa ta yi watsi da kuduri mai lamba 2303 na kwamitin sulhu na MDD, da aka cimma a ranar 29 ga watan Yuli, dake ba da hurumin tura 'yan sandan MDD 228 a Bujumbura da ma a wasu yankuna 17 na kasar Burundi.

Gwamnatin Burundi ta yi watsi da dukkan matakan kudurin dake da nasaba da batun tura duk wata runduna a kasarta, dake sabawa duk wasu dokokin MDD, da kuma suke take 'yancin kasarta, in ji Philippe Nzobornariba, kakakin gwamnatin Burundi, kana sakatare-janar na gwamnati, a kafofin gidan rediyo da talabijin na kasar Burundi.

Mista Nzobonariba ya yi alla wadai da cewa kwamitin bai yi la'akari da matsayin Burundi ba.

A cikin sanarwar, gwamnatin Burundi ta soki kasar Faransa da take zargi da neman janyo bala'in kisan kiyashi zuwa kasar Burundi a yayin da batun yiyuwar hannunta a cikin wannan bala'in ba a kawar da shi ba.

Ya kara da cewa Faransa ta manta da ci gaban da ake samu ta fuskar matsalar tsaro a Burundi.

Kudurin na ba da damar tura wani adadin 'yan sandan MDD 228 a kasar Burundi, tare da muhimmin aikin sanya ido kan matsalar tsaro da kuma bayar da rahoto ga sakatare janar na MDD.

Mambobi goma sha daya na kwamitin sulhu suka jefa kuri'u game da wannan kuduri, tare da bayyana wajabcin yin rigakafin tashe tashen hankali a Burundi.

A yayin da kasashen Masar, Sin, Venezuela da Angola suka janye jiki ga zaben tare da bayyana cewa kudurin bai samu goyon baya tun farko daga hukumomin Burundi ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China