An dai gudanar da zanga zangar ne a manyan titunan Bujunbura, babban birnin kasar, domin nuna bacin ransu game da abin da suka kira Faransa tana tsokanarsu, saboda gabatar da kuduri a gaban kwamitin sulhu na MDD na neman tura dakaru zuwa kasar.
Dubban 'yan kasar sun taro a ofishin jakadancin Faransa dake kasar, inda suke bayyana cewa ba za su amince 'yan kasashe waje su shiga Burundi ba muddin suna raye, kuma ba za su amince Faransa ta zaba musu shugaban kasa ba.
Da yake tsokaci, magajin garin Bujunbura Freddy Mbonimpa ya ce, daga cikin makasudin zanga zanagar shi ne domin nunawa kafafen yada labaru na cikin gida da na kasashen waje cewa, kasar Burundi tana zaune lafiya, kuma tana da 'yancin kanta, kana ba ta bukatar a turo mata wasu dakaru daga kasashen waje, kuma suna bukatar Faransa da ta dakatar da tsokanar da take yiwa kasar. (Ahmad Fagam)