Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da hare-haren Boko Haram, ya bayyana cewa, hare-haren da mayakan Boko Haram suke kaddamarwa a wasu sassan jihar ba sa razana shi ko kadan.
Da yake yiwa manema labarai karin haske a garin Bama, birni na biyu mafi girma bayan Maiduguri, babban birnin jihar, gwamna Shettima ya ce, zai ci gaba da shirin sake gina garin, tun bayan da mayakan na Boko Haram suka kona shi kurmus.
Gwamna Kashim Shettima ya yi wadannan kamalai ne a lokacin da ya ke mayar da martani game da hare-haren baya-bayan nan da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kauyukan Logumani da Dara/Jamal wadanda ke kan iyaka, hare-haren da suka yi sanadiyar halaka wani jami'in soja 1 da kuma wasu kuratan sojoji biyu.
Tun a ranar Larabar makon da ya gabata ne dai gwamnan ya mayar da ofsihinsa zuwa garin na Bama, domin fara aikin sake ginawa da gyara gidaje sama da 2,500 da shaguna da gine-ginen gwamnati da Boko Haram suka lalata a shekarar 2014.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, babu abin da mayakan Boko Haram suke yi, illa cusa tsoro a zukatan jama'a. A saboda haka ya ce, lokaci ya yi da jama'a za su jajurce, su yaki wadanda ke kokarin lalata musu rayuwa da dukiyoyi a jihar, da ma daukacin shiyyar baki daya.
Gwamnan ya ce, mayar da ofshinsa zuwa garin na Bama, wata alama ce da ke nuna cewa, an ci karfin kungiyar ta Boko Haram.(Ibrahim)