in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram a kalla 22
2016-09-26 10:02:08 cri

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunta sun yi nasarar halaka a kalla mayakan Boko Haram 22, yayin wani farmaki da suka kaddamar a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da kakakin sojojin Najeriyar Kanar Sani Usman ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa, hudu daga cikin sojojinsu sun mutu a lokacin da suke mayar da martani ga harin mayakan na Boko Haram, kana biyu kuma suka ji rauni.

Ya ce, sojojin sun yi aranga da mayakan Boko Haram har sau uku, inda suka yi amfani da gurneti da makaman harba rokoki 36 a garin Logomani. Haka kuma sojojin sun yi nasarar kwato kurtun harsasan bindiga kirar AK-47,da na bindiga kirar G3 guda 1 da kuma wasu gurnetin 36.

Kanar Usman ya ce yanzu haka an kara tsaurara matakan tsaro a yankin, yayin da dakarun Najeriyar ke ci gaba da aikin kakkabe mayakan na Boko Haram.

Yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriyar dai ya kasance tungar kungiyar Boko Haram. Ko da yake a watannin baya, mahukuntan Najeriya sun sha kaddamar da hare-hare domin kawar da barazanar da 'yan ta'adda ke haifarwa a yankin da ma sauran sassan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China