in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da shiga aikin MDD na kiyaye zaman lafiya
2016-06-03 20:15:10 cri

Bayan aukuwar harin ta'addanci kan sojojin kasar Sin dake aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar daya daga cikin sojojin, yayin da wasu suka jikkata, wasu sun fara nuna damuwar cewa, ko kasar ta Sin za ta ci gaba da shiga aikin MDD na kiyaye zaman lafiya a nan gaba?

Dangane da hakan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kasar Sin na da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, wanda hakan babban nauyi ne da aka dora mata. kuma Sin na sauke wannan alhaki yadda ya kamata. Madam Hua wadda ta yi wannan tsokaci a yau Jumma'a yayin wani taron manema labarai a nan birnin Beijing, ta kara da cewa nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da shiga aikin MDD na kiyaye zaman lafiya, tare da tabbatar da ganin MDD ta taka muhimmiyar rawa a al'amuran kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China