Mr. Ban ya bayyana haka a yayin da yake yin jawabi a jami'ar manajoji ta Singapore, a yayin da yake tsokaci kan batun da ke jawo hankalin al'umma a shiyyar, ya ce, ana nuna damuwa da yanayin tekun kudancin kasar Sin sosai, sabo da sabani da rashin fahimtar juna a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa, lamarin da kuma zai iya kawo illa ga zaman lafiyar yankin.
Bugu da kari, ya ce, ya yi ta yin kira ga bangarorin da abin ya shafa su warware sabanin dake tsakninsu ta hanyar yin shawarwari kuma bisa dokokin kasa da kasa, yana kuma fatan bangarorin daban daban da batun tekun kudancin kasar Sin ya shafa za su iya kara fahimtar juna a tsakaninsu ta hanyar tsara ka'idojin tekun kudancin kasar Sin yadda ya kamata. (Maryam)