Tawagar kungiyar manoman Guinea-Bissau (ANAG) za ta kawo ziyarar kasar Sin domin kammala sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da takwarorinsu na kasar Sin, in ji shugaban kungiyar James Gomes a ranar Talata.
Mista Gomes ya bayyana cewa wannan yarjejeniyar ta kunshi wani tallafin kasar Sin wajen horar da kuma samar da kayayyakin aiki gona ga kungiyar ANAG.
A shekarar 2015, manoma da kwararru Guinea-Bissau fiye da 60 suka samu horo a nan kasar Sin, domin samun damar kara kyautata bunkasa noma a kasar Guinea-Bissau, in ji mista Gomes.
Kungiyar ANAG na fatan samun na'urorin noma domin bunkasa noma a Guinea-Bissau, inda har yanzu kusan kashi 90 cikin 100 na manoman kasar suke aikin noma a gargajiyance. Gomes ya kara da cewa, suna iya kara bunkasa samar da albarkatun noma bisa hulda da kasar Sin, sakamakon kasancewar kasarsa a matsayin wata kasa ta noma. (Maman Ada)