in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana za ta tara sama da dala biliyan 4 a kasuwar takardun bashi na cikin gida
2016-08-30 11:18:35 cri
Rahotanni daga kasar Ghana na cewa, daga watan Agusta zuwa Disamban wannan shekara, gwamnatin kasar za ta tara kudaden da yawansu ya kai a kalla dala biliyan 6.4 kwatankwacin kudin kasar Cedi biliyan 25.3 daga cinikin takardun bashi na cikin gida.

Babban bankin kasar shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin. Yana mai cewa, za a yi amfani da kudaden takardun bashin da aka sayar wajen biyan basussukan da ake bin kasar da yawansu ya kai dala biliyan 6.04. kana ragowar dala miliyan 358.8 kuma za a yi amfani da su wajen tafiyar da harkokin kudin gwamnati.

Bayanai na nuna cewa, za a rika sayar da takardun bashi masu wa'adin kwanaki 91 da kwanaki 182 ne mako-mako, yayin da takardun bashi masu wa'adin shekara guda kuma za a rika sayar da su bayan makonni bibbiyu, kuma za a yi hakan ne ta hannu kananan dillalan masu sayar da takardun bashi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China