A wata sanrwar da shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar ta GIS Francis Palmdeti ya fitar, ta ce, tuni aka fara gwajin wannan sabon tsari a filin jirgin sama na Kotoka dake birnin Accra tsawon watanni uku, daga bisani za ta fadada shirin zuwa dukkan hanyoyin shiga kasar.
Wannan mataki na ba da takardun izini da gwamnatin kasar Ghana ta bullo da shi, cika alkawari ne na yarjejeniyar da aka cimma a taron shugabannin kungiyar AU a farkon wannan shekara a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Mambobin kungiyar kasashen AU sun bullo da wannan shiri ne, a matsayin daya daga cikin hanyoyin tabbatar da tsaro a ciki da wajen kasashen nasu, inda sabon shirin zai ba da takardun izinin zama a kasashen na tsawo kwanaki 30 ga 'yan kasashen da suka fito daga kasashe mambobin kungiyar.
Ghana ta kasance kasa ta farko da ta fara aiwatar da sabon tsarin, inda ta samu lambar yabo daga kungiyar tarayyar Afrika AU. (Ahmad Fagam)