Rahotanni daga kasar Ghana na cewa, jam'iyyun siyasun kasar sun amince su sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta tabbatar da gudanar da zabukan kasar na watan Disamba a wannan shekara cikin nasara.
Wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da yammacin Afirka Dr. Ibn Chambas ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a karshen mako bayan da ya jagoranci wata tawaga mai mutane biyar daga kungiyar ECOWAS da kungiyar tarayyar Afirka wato AU da MDD wadda ke rangadin kwanaki uku a kasar ta Ghana.
Dr. Ibn Chambas ya ce, manufar ziyarar tawagar ita ce, nanata goyon bayan al'ummomin kasashen duniya game da bukatar gudanar da zabukan kasar cikin lumana, gaskiya da kuma adalci.
Ya kuma shaida wa manema labarai cewa, za a sanya hannu kan wannan yarjejeniya ce a bainar jama'a da 'yan kallo na kasa da kasa da suka kunshi, kungiyar ECOWAS, AU da kuma MDD. Ya ce, yana fatan cewa, dukkan jam'iyyun siyasun kasar za su martaba tanade-tanaden da ke kunshe cikinta a lokacin yakin neman zabe da ma ragowar harkokin da suka shafi zabukan.
Sauran muhimman fannonin da ake fatan yarjejeniyar za ta magance sun hada da rikice-rikicen zabe da bukatar bullo da wasu matakai don kara tattaunawa da fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki da nufin warware duk wasu matsalolin da suka kunno kai.
A saboda haka, ya yi kira ga hukumar zabe, da bangaren shari'ar kasar ta Ghana da su mutunta zabin al'ummar kasar.
A ranar 7 ga watan Disamba a wannan shekarar ce za a gudanar da zaben shugaban kasa, inda za a fafata tsakanin jam'iyyar NDC mai mulki da babbar abokiyar hamayyarta wato NPP. (Ibrahim)