in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mo Farah ya kare kambin sa a gasar gudun yada kanin wani ta "Great North"
2015-09-17 13:21:22 cri
A ranar Lahadi 13 ga watan nan ne aka gudanar da gasar tseren gudun yada kanin wani ta kasar Birtaniya, gasar da Mo Farah ya sake cimma nasarar lashe manyan lambobin yabo a cikin ta. Ita dai wannan gasa ta Marathon wadda ake gudanarwa ana tsere ne na rabin zango a cikin ta.

A kuma wannan karo Mo Farah, wanda ya lashe tseren mita 5000 da na mita 10,000 a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da ta gudana 'yan kwanakin baya a birnin Beijing, ya sake kare matsayin bajimtar sa a gasar ta Birtaniya.

Dan wasan mai shekaru 32 da haihuwa ya kammala gudu cikin mintoci 59 da dakika 22, inda ya zama mutum mafi sauri a duk kasar sa ta Birtaniya a wannan fage bisa tarihin gasar.

A daya bangaren kuma Mary Keitany 'yar kasar Kenya ce ta sake cimma nasarar lashe gasar ajin mata, bayan da ta kammala gudu cikin sa'a 1 da mintoci 7 da dakika 32, inda ta tserewa abokiyar karawar ta Gemma Steel daga kasar Birtaniya da mintuna 3 da rabi.

Wani dan wasan gudun yada kanin wani ya mutu a yayin da yake halartar gudun Marathon na rabin zango na Great North a birnin Newcastle. Masu shirya gasar gudun sun bayyana alhinin su ga rasuwar dan tseren, sun kuma jajantawa iyalai da abokan arzikin sa.

Mutane kimanin dubu 57 ne suka halarci gudun yada kanin-wani na "Great North" na rabin zango a wannan karo, wanda aka gudanar daga birnin Newcastle zuwa South Shields.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China