Mr. Alfred Schipke ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing, inda ya ce, bisa sabon rahoton da IMF ta fitar game da bincike kan halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, sabon shirin shekaru biyar da Sin ta tsara ya tabbatar da buri mai ma'ana, wanda ya kunshi yadda kasar ta samu babban ci gaba wajen gudanar da kwaskwarima a fannonin manufofin kudi, da raya garuruwa da dai sauran su. Baya ga haka ta yi nasara wajen daukar matakai na rage kayayyakin da ake samarwa wadanda suka wuce kima, da ma gudanar da kwakwarima kan masana'antun mallakar gwamnati da dai sauransu. (Bilkisu)