in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen waje na matsayi na 2 a duniya
2016-09-22 15:28:43 cri
Zhang Xiangchen, mataimakin wakili mai kula da batun shawarwari kan cinikayyar kasa da kasa na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya furta a yau Alhamis cewa, a shekarar 2015, kasar Sin ta sami ci gaba sosai a fannin zuba jari ga kasashen waje, inda yawan jarin da ta zuba ya kai dalar Amurka biliyan 145.67, sakamakon saurin karuwar adadin cikin shekaru 13 a jere. Haka kuma, adadin na yanzu, a cewar jami'in, yana matsayi na biyu a duniya.

Zhang ya fadi haka ne a wajen taron manema labaru da ofishin kula da watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira, inda ya ce a shekarar 2015, kudin da kasar Sin ta zuba ma ketare ya fi jarin da ta janyo daga kasashen waje yawa. Haka zalika, bisa rahoton da aka gabatar game da yanayin harkar zuba jari ga kasashen waje na kasar Sin, kudin da Sin ta zuba wa waje a bara ya karu da kashi 18.3%, wanda ya kai kashi 9.9% cikin dukkan kudin jarin da aka zuba a kasashe daban daban na duniya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China